Isa ga babban shafi
Turai

Kasashen Turai sun ki karban 'Yan gudun hijira

Kasashen gabashin nahiyar Turai sun ki amince wa da bukatar Kasar Jamus na su karbi baki yan gudun hijira yayin da wani hoton boidiyo ke nuna yadda ake muzgunawa bakin a Kasar Hungary.

Dubban bakin-haure ne ke ci gaba da kwarara zuwa Turai yawancinsu mutanen Syria
Dubban bakin-haure ne ke ci gaba da kwarara zuwa Turai yawancinsu mutanen Syria REUTERS/Dimitris Michalakis
Talla

Har ila yau Kasar ta Hunagry ta bayyana cewa daga mako mai zuwa za ta fara kama duk wanda ya tsallako cikin Kasar ba bisaka’ida ba.

A wani taro da ministocin harkokin wajen Kasashen Turai suka gudanar a birnin Prague na Jamhuriyar Czech, Ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier ya gargadi takororinsa cewa matsalar kwararar dubban Yan gudun hijira na iya zama babban kalubale ga nahiyar Turai a tarihi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.