Isa ga babban shafi
Turai

Ministocin Turai za su tattauna batun rarraba bakin haure

Ministocin harkokin cikin gida na kungiyar kasashen Turai za su gudanar da wani taro a Brussels kan batun rarraba bakin haure a tsakaninsu. Wannan na zuwa ne a yayin Jamus ta tsaurara matakai akan iyakokinta domin rage kwararar bakin zuwa cikin kasar.

Daruruwan 'Yan ci-rani na cin abinci a Jamus
Daruruwan 'Yan ci-rani na cin abinci a Jamus
Talla

Dubban ‘Yan gudun hijirar Syria da baki ‘Yan ci rani ne ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai.

Kasashen za su tattauna yadda za su rarraba bakin haure kimanin 160,000 a tsakaninsu, musamman wadanda suka tsallako zuwa kasashen Italiya da Girka da Hungary da ke gabar ruwan Mediterranean.

Taron kuma zai yi kokarin magance matsalar kasashen da ke Gabashin Turai wadanda ke ci gaba da bayyana adawarsu da shirin rarraba bakin hauren.

Kasashe irinsu Slovakia da Jamhuriyar Czech na cikin kasashen da ke sahun gaba da ke adawa da shirin rarraba bakin hauren tsakaninsu.

Kwamishinan kula da hijira da ayyukan cikin gida na Tarayyar Turai Dimitris Avramopoulos ya ce ya zama wajibi ga kasashen sun hada kai idan suna son magance matsalar bakin-haure da ke ci gaba da kwarara a Turai.

Hukumar za ta gabatar da adadin ‘Yan gudun hijirar da kowace kasa za ta karba tsakanin mambobin kungiyar.

Jamus ta amince za ta karbi kashi 20 na ‘Yan gudun hijirar Syria kimanin 31,400.
Faransa ma ta amince za ta karbi 24,000, Birtaniya 20,000, yayin da Spain ta amince ta karbi 14,900.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.