Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta nada Minista kan ‘Yan gudun hijirar Syria

Gwamnatin Birtaniya ta nada Minista na musamman domin kula da ‘Yan gudun hijira kimanin 20,000 ta kasar ta yi alkawalin za ta karba daga sansaninsu da ke kasashen da ke makwabtaka da Syria a shekaru 5 ma su zuwa.

Firaministan Birtaniya David Cameron ya kai ziyara sansanin 'Yan gudun hijirar Syria a tsaunin Bekaa a kasar Lebanon
Firaministan Birtaniya David Cameron ya kai ziyara sansanin 'Yan gudun hijirar Syria a tsaunin Bekaa a kasar Lebanon REUTERS
Talla

Firaministan kasar David Cameron ya nada Richard Harrington domin kula da ayyukan ‘Yan gudun hijirar na Syria.

Cikin sanarwar da ofishin Firaministan ya fitar, sanarwar ta ce Ministan zai kula da tsara yadda gwamnati za ta yi hidima da ‘Yan gudun hijirar 20,000 na Syria.

A yau Litinin Firaministan Birtaniya David Cameron ya kai ziyara sansanin ‘Yan gudun hijirar Syria a Lebanon domin ganewa idonsa  halin da ‘Yan gudun hijirar ke ciki.

Birtaniya dai na cikin manyan kasashen da ke bayar da tallafi wajen kula da ‘Yan gudun hijirar Syria, kuma a ziyarar da ya kai sannan ‘yan gudun hijirar a Lebanon, David Cameron ya ce kasarsa za ta ci gaba da bayar da tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.