Isa ga babban shafi
Faransa-Isra'ila

Faransa na goyon baya yiwa kayyakin Yahudawa 'yan share waje zauna alama

Faransa tace tana goyon bayan shirin Kungiyar taraiyyar Turai ta EU, na yin alama kan dukkan kayayyakin da aka shigar dasu daga yankunan yahudawa ‘yan share waje zauna a kasar Isra’ila.

Ministan tattalin arzikin Faransa Emmanuel Macron
Ministan tattalin arzikin Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Charles Platiau
Talla

Sai dai mahukuntan na birnin Paris sun bayyana adawa da kiran da ake yi na kauracewa kayayyakin da ake yi a Isra’ilan.
Lokacin da yake ziyara a kasar Isra’ila da yankuna Falasdinu, Ministan tattalin Arzikin Faransa Emmanuel Macron yace matsayin Diplomasiyya da Faransa da Taraiyyar Turai suka dauka kan lamarin a bayyane suke, basu canza ba kuma ba zasu canza ba.
Dama Isra’ila ta caccaki matakin yiwa kayayyakin alama, inda tace wani yunkuri ne na haramta mata cinikinsu.
Sai dai Macron yace Faransa bata goyon bayan kiraye kirayen da Falasdinawa keyi na kauracewa, da sanya takunkumi kan kayayyakin, matakan da take son ayi amfani dasu na siyasa da tattalin arziki, don matsin lamba ga Isra’ila kan mamayar data yiwa yankunansu.
Cikin watan Aprilu, Faransa da wasu kasashen EU suka yi kiran ayi alama kan kayayyakin da ake sayar musu, da suka fito daga yankunan Falasdinawan da Isra’ila ta mamaye a gabashin Jerusalem da Tiddan Golan, a lokacin yakin da akayi na kwanaki 6 a shekarar 1967.
Dama Faransa ta bayyana mamayar a matsayin barazana ga zaman lafiyan gabas ta tsakiya da kokarin samar da kasar Palasdinu mai cin gashin kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.