Isa ga babban shafi
Faransa

Ana farautar wasu 'yan fashi a Faransa

‘Yan Sandan Kasar Faransa suna can suna farautar wasu ‘yan fashi da makami, da suka tsere bayan aikata sata a wani shagon sayar da kayayaki a birnin Paris.Zuwa yanzu jami’an rundunar musamman sun shiga aikin farautar mutanen, tare da killace yankunan da ake zargin sun boye.

Jami'an 'Yan Sandan Faransa
Jami'an 'Yan Sandan Faransa AFP PHOTO / LOIC VENANCE
Talla

Mutanen 3 da ake tunanin daya daga cikinsu ma’aikacin shagon da aka yi fashin ne, sun afka shagon Primark dauke da bindigogi, tare da umartar jama’a su tsaya inda suke, yayin da kuma wasu suka boye don radin kansu.

Wata ma’aikaciyar shagon ce ta fara sanar da saurayinta abinda ke faruwa ta hanyar sakon kar ta kwanan wayar hannu wato Text Message, inda ta shaida masa cewa wasu mutane sun yi garkuwa da su.

Cikin kankanin lokaci aka sanar da ‘yan sanda, inda su kuma suka killace yankin, aka dakatar da ababen hawan dake zuwa wurin, tare da rufe dukkan shagunan da ke kusa, kafin ‘yan sanda su garzaya wajen da aka yi garkuwar.

Bayan jami’an tsaro sun ceto mutanen an yi tunanin ‘yan fashin na cikin shagon, amma kuma sai aka gano sun tsere.

Masu gabatar da kara sun ce da alama mutanen ba su kwashi kudade ba, tsawon lokacin da suka kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.