Isa ga babban shafi
Girka

'Yan Majalisu a Girka sun amince da bukatar karbar tallafi a karo na uku

Majalisar dokoki a Girka ta amince da sabon yarjejeniyar ceto kasar daga kangin bashi, bayan shafe dare ana muhawara a tsakanin ‘yan majalisun kasar.

Ministan Girka Alexis Tsipras a Majalisa
Ministan Girka Alexis Tsipras a Majalisa Reuters/路透社
Talla

‘Yan Majalisu sun nuna goyon baya ga sabbin matakan ceto tattalin arzikin Kasar dake cikin wani hali sai dai akasarin ‘Yan majalisun karkashin jam’iyyar syriza sun nuna rashin amincewarsu da tsarin.

Sabbin matakan dai sun kunshi Karin kudaden haraji da kuma tsuke bakin aljihun gwamanti kafin Kungiyar Tarayyar Turai ta baiwa Girkan wani bashin a karo na uku da ya kai Euro biliyan 85 cikin shekaru biyar.

A bangare guda, ministocin kasashe masu amfani da takardar kudin Yuron sun taru a yau a birnin Brussels na Kasar Belgium domin kada kuri’ar amincewa da wannan tsarin.

An dai bukaci tsarin ne domin taimakawa Girka ci gaba da kasancewa a cikin jerin kasashe masu amfani da kudin Euro kuma a ceto ta daga matsalar bashin da ya yi mata katutu.

To sai dai hakan na a matsayin wani kalubale ga Firai Ministan Kasar Alexis Tsipras ganin yadda ‘Yan Majalisun dokoki 40 karkashin jam’iyyar Syriza suka nuna adawarsu a gare shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.