Isa ga babban shafi
Girka

IMF ta soki Tarayyar Turai akan Girka

Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta ce Girka na bukatar kudade fiye da Dala Biliyan 86 domin ceto tattalin arzikin kasar da bashi ya yi wa katutu. Wannan ne zuwa ne a yayin Majalisar kasar Girka za ta kada kuri’ar amincewa ko kuma yin watsi da yarjejeniyar sabbin tsare tsare da ma su bin kasar suka shata domin samun Karin kudaden tallafin.

Firaministan Girka Alexis Tsipras.
Firaministan Girka Alexis Tsipras. REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

IMF ta ce ya kamata kungiyar Tarayyar Turai ta sauya matsayinta akan wa’adin da suka ba Girka.

Yanzu haka Firaministan Girka Alexis Tsipras na fuskantar adawa daga wani bangare na Jam’iyyar Syriza mai mulki.

Kungiyar kasashen Turai da hukumar bada lamuni ta duniya sun yi gargadi akan Girka na matukar bukatar kudaden Tallafi domin kaucewa ficewa daga kungiyar kasashe da ke amfani da kudin yuro.

Amma Al’ummar Girka da dama sun bayyana bacin ran su da yarjejeniyar wacce za ta tilastawa gwamnati aiwatar da wasu sauye sauye masu tsauri da suka hada da dokar kwadago da fansho da haraji.

Sai dai kuma Firaminsitan Alexis Tsipiras ya dauki alhakin kulla yarjejeniyar duk da ya ke yace bai amince da wasu daga cikin bukatun ma su bin kasar bashi ba.

Amincewar majalisar ne zai sa shugabanin kungiyar kasahsen Turai su fara tattaunawa kan kudin da za a ba kasar da suka kai euro biliyan 86.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.