Isa ga babban shafi
Girka

Kungiyoyin kwadago a Girka za su tsuduma yajin aiki

Shugaban Faransa François Hollande ya bayyana manufar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Girka da kasashen Turai na yankin kudin Euro, bayan da Hukumomin Girka dake halartar tattaunawar suka nuna amincewa kan batun tada komadar tattalin arzikin da kasashen Turai tare da hukumomin bayar da Lamani na duniya suka gindaya mata.

Shugaban Faransa  Francois Hollande  a zauren tattaunawa kan batun Girka
Shugaban Faransa Francois Hollande a zauren tattaunawa kan batun Girka Reuters/Francois Lenoir
Talla

Shugaba Hollande da babbar murya ya bayyana wanan yarjejeniya zuwa kasar Girka a matsayi wata damar ci gaba da kasancewa a gungun masu amfani da kudaden Euro, wannan ita ce manufar, ta hanyar mutunta tsarin da kasashen turai suka shinfida.
Manufarmu ita ce ganin yankin kasashen dake amfani da kudaden Euro sun ci gaba da kasancewa a dunkule, waje guda da kuma zumuntar dake tsakaninsu, inji Shugaba Francois Hollande.

Manufarmu kasashen Turai ita ce sake taimakawa kasar Girka , bayan tsawon shekaru tana fama da wahalhalu tare da tsuke bakin aljihu, duk da cewa har yanzu ba wai girkan ta rabu da su bane, wanda ya kamata ta kara ko kari a kai.

Yana da matukar muhimmanci ministocin kudin yankin Euro sun samar da hanyoyin da zasu kai ga baiwa Girkar kudade inji Shugaban kasar Faransa Francois Hollande.
Yanzu haka rahotani daga kasar ta Girka na nuni da cewa kungiyoyin kwadagon kasar sun sanar da fara yajin aiki daga gobe talata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.