Isa ga babban shafi
Girka

Girka ta cim ma yarjejeniya da kasashen Turai

Kasar Girka mai fama da dimbin bashi ta cim ma yarjejeniya da kasashen da ke amfani da takardar kudin yuro a yau Litinin, bayan bangarorin biyu sun shafe dare suna tattaunawa.

Firaministan Girka Alexis Tsipras tare da shugabannin kasashen Turai
Firaministan Girka Alexis Tsipras tare da shugabannin kasashen Turai (©Reuters)
Talla

Hakan na nufin Firaministan Girka Alexis Tsipras ya amince da bukatun Turai na tsauraran matakan tsuke bakin aljihun gwamnati domin samun kudaden tallafi da suka kai yuro biliyan 86.

Wannan Matakin dai zai hanawa Girka ficewa daga kungiyar kasashen da ke amfani da kudin yuro.

Girka ita ce kasa ta farko daga cikin kasashen da suka ci gaba da ta gaza iya biyan bashin da ake bin ta kuma wannan ne karo na uku da kasar ke samun kudaden Tallafi cikin shekaru biyar.

An shafe tsawon makwanni biyu Bankunan kasar Girka na rufe, matakin da gwamnatin kasar ta dauka saboda rashin samun Karin tallafi daga kungiyar Tarayyar Turai.

An shafe tsawon watanni shida Kasashen Turai na tattaunawa da gwamnatin Tsipras da ke adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, lamarin da ya jefa kasashen Turai da ma su bin kasar bashi cikin fargaba.

Tun lokacin da aka zabi Firaminista Alexis Tsipras, kasar Girka ta shiga takun-saka da masu bin ta bashi, da suka hada da Asusun lamani na Duniya IMF, da Babban Bankin Turai sakamakon lasar takobin da ya yi na kawo karshen shirin matse bakin aljihun, da aka faro tun cikin shekarar 2010.Girka ta samu Karin tallafin bashin ne bayan

Shugabannin Jamus da Faransa da kungiyar kasashen Turai sun gabatar da wani shirin hadin gwuiwa kan yadda za’a tallafawa kasar da wani sabon bashi.

Tuni dai Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa kasar shi za ta yi duk abin da za ta yi don ganin Girka ba ta fice daga cikin kasashe ma su amfani da kudin Yuro ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.