Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Girka ta gabatar da sabbin matakan ceto tattalin arzikinta

Kasar Girka ta gabatar da sabbin tsare tsaren ceto tattalin arzikinta ga Kasashe masu amfani da kudin Euro yayin da Faransa da Italiya suka bayyana gamsuwarsu da sabbin matakan.

Alexis Tsipras a gaban 'yan  majalisar dokokin Girka
Alexis Tsipras a gaban 'yan majalisar dokokin Girka REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Kasashen na Faransa da Italiya sun nuna farin cikinsu da sabbin matakan da Girka ta gabatar na ceto kanta daga kangin bashi kuma sun samu kwarin gwiwar cewa , matakan zasu taimaka wajan kai ga cimma yarjejeniya da zata hana Girka ficewa daga kasashen Turai.

Tuni dai Kungiyar tarayyar turai da asusun bada lamuni na duniya harma da babban bankin turai suka yi nazari kan wadannan matakan da gwamanatin Firai ministan Girka Alexis Tsipras ta gabatar.

To sai dai a yau jumma’a ne za a gabatar wa ‘yan majalisar dokokin Girka sabbin matakan domin kada kuri’ar amincewa da su.

A cikin sabbin matakan dai Tsipras ya taba batun haraji da za a kara da kuma kudin Pansho da za a gyara tare da takaita kudaden da ake kashe wa sojoji, lamarin da ya karfafa gwiwar Faransa da ta kasance kawa ga Girka, inda Shugaban Kasar Francois Hollande yace, Girka ta nuna alamar san ci gaba da zama a jerin kasashe masu amfani da kudin Euro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.