Tarayyar Turai ta ba Girka tallafin gaggawa
Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da tallafin gaggawa na kudi sama da yuro Biliyan 7 ga Girka domin kasar ta samu damar biyan dimbin basussukan da hukumar lamuni ta duniya ke bin ta.
Wallafawa ranar:
Matakin ba girka tallafin gaggawa ya samu amincewar mambobin kungiyar Tarayyar Turai 28, kamar yadda mataimakin hukumar ya tabbatar.
Girka dai na bukatar tallafi ne domin biyan hukumomin da ake bin kasar bashi da suka hada da babban bankin Turai da asusun Lamuni.
Girka za ta yi amfani da wannan Tallafin domin biyan babban Bankin Turai bashin kudi sama da yuro biliyan 4 kafin wa’adin da aka dibarwa kasar ya cika a ranar Litinin.
Wannan kuma na zuwa ne a yayin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu goyon bayan majalisar kasar kan kudirin tallafawa kasar Girka da bashin kudi.
Idan dai Girka ta kammala biyan sauran bashin, zata fara samun sabbin tallafi karkashin tsarin dadaito na kungiyar Tarayyar Turai
Sai dai bashin da Girka ta samu yanzu na tsawon watanni uku ne amma dama ce na samun kudade da za ta tafiyar da wasu harkokinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu