Isa ga babban shafi
Girka-EU

Majalisar Girka ta amince da yarjejeniyar bashin Turai

Majalisar Kasar Girka ta amince da yarjejeniyar bai wa kasar bashi da aka kulla da kungiyar kasashen Turai mai tattare da sarkakiya bayan an dauki dogon lokaci ana tafka mahawara mai zafi.

Firaministan Girka Alexis Tsipras a zauren Majalisa
Firaministan Girka Alexis Tsipras a zauren Majalisa REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Firaministan Girka Alexi Tsipiras ya yi nasarar samun goyan bayan majalisar bayan ‘Yan Majalisu sun caccaki yadda ya bada kai kungiyar kasashen Turai ta hau kansu akan shirin tallafawa kasar, saboda tsaurin sharadodin da aka gindayawa a cikin yarjejeniyar.

‘Yan Majalisu 229 suka goyi bayan shirin wanda ya kunshi Karin haraji da shekarun aiki da kuma dokar fansho daga cikin Majalisar mai wakilai 300.

Mutanen Girka sun yi arangama da jami'an tsaro domin nuna adawa da amincewa da yarjejeniyar Turai
Mutanen Girka sun yi arangama da jami'an tsaro domin nuna adawa da amincewa da yarjejeniyar Turai REUTERS/Yannis Behrakis

Da wannan nasara yanzu Firaminsitan Girka zai fuskanci kungiyar kasashen Turai da Babban Bankin Turai a karshen wannan mako don amincewa da shirin yadda za a mikawa kasar tallafin da ya kai yuro biliyan 86.

A lokacin da majalisar ke zama a jiya Laraba, masu zanga-zanga sun mamaye titunan birnin Athens suna kona tayun mota tare da yin aranagama da ‘Yan Sanda don nuna adawar su da shirin tallafin.

Mutanen Girka za su fuskanci matsi na matakan tsuke bakin aljihun gwamnati anan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.