Isa ga babban shafi
Faransa-Girka

Hollande ya ce akwai darasi a yarjejeniyar Girka da kasashe masu amfani da Euro

Shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana yarjejeniyar da kasar Girka ta cimma da kasashen dake amfani da kudin Euro da cewa, bata ci fuskar kasar ta Girka ba, dangane da dimbin bashin dake daddale a kan kasar.

Shugaban Faransa François Hollande a wani taro a Brussels kan Girka.
Shugaban Faransa François Hollande a wani taro a Brussels kan Girka. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaba Hollande yace daga cikin darussan da aka tsinka a rikicin tattalin arzikin kasar ta Girka, Faransa zata gabatar da shawarwarin samar da gwamnatin da zata mayar da hankali kan shi’anin da ya shafi tattalin arziki a nahiyar Turai.

A yayin jawabin a wata tattaunawa ta Tv albarkacin zagayowar ranar shagulgulan kasa na ranar 14 ga watan Yuli a jiya talata, shugaba Hollande ya ce shi ba zai taba amincewa a ci zarafin al’ummar wata kasa ba, wanda yace cin zarafin shine a kori Girka daga cikin jerin kasashen dake amfani da kudin Euro a nahiyar Turai, saboda ta kasa cika sharuddan biyan bashin dake dankare a kanta.

Sai dai kuma Hollande ya ki ya bayyana cewa ko shawarwarin da Faransa ta bayar ne suka yi nasarar cimma yarjejeniya da kasar Girka, amma ya ci gaba da cewa, gaba daya nahiyar turai ce ta yi nasara, ita kuma Faransa ta taka duk wata rawar da ya kamata ta taka ne da ya kai ga cimma yarjejeniyar.

Sai dai kuma shugaban kasar ta Faransa ya ci gaba da cewa in bacin hadin gwiwar kasashen Faransa da Jamus da ba’a cimma yarjejeniyar ta tarihi da kasar Girka ba, a cewarsa .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.