Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Bankin Turai ya ce Girka ba za ta samu karin rance ba.

Babban Bankin Turai ya yanke shawarar kin kara yawan kudi rancen gaggawa ga kasar Girka, inda ya ce zai tsayar da tallafin kan matakin da aka tsayar a ranar Juma'ar da ta gabata.

Firai ministan Girka Alexis Tsipras.
Firai ministan Girka Alexis Tsipras. REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Matsayin da bankin ya dauka, ya biyo bayan kasa cimma dai-daito a tattaunawar da aka yi tsakanin Girka da kasashe masu amfani da kudin euro a kan yarjejeniyar tallafin ceto wanda kecika a ranar Talata mai zuwa.

Wannan dai na zuwa ne, bayan Majalisar dokokin Kasar ta amince da kada kuri’ar raba gardama kamar yadda Firayi Ministan Kasar Alexis Tsipras ya bukata a game da sabon tsarin ceto Kasar daga kangin bashin da ake binta.

'Yan majalisar dokokin 179 ne cikin 300 suka amince da wannan kuri’ar da za a gudanar a ranar 5 ga watan Yuli mai zuwa.

A ranar talata mai zuwa ne aka bukaci Girka ta biya asusun bada lamuni na duniya dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 800.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.