Isa ga babban shafi
Girka-EU

Tarayyar Turai ta kira taron gaggawa kan Girka

Kungiyar Tarayyar Turai ta kira taron gaggawa a makon gobe domin tattauna yadda za shawo kan matsalar Girka bayan sun kammala tattaunawa a ranar Alhamis ba tare da cim ma matsaya ba kan kudaden tallafin da za a ba kasar.

Firaministan Girka Alexis Tsipras tare da Shugaban hukumar Turai  Jean-Claude Juncker a Brussels, Belgium
Firaministan Girka Alexis Tsipras tare da Shugaban hukumar Turai Jean-Claude Juncker a Brussels, Belgium Reuters
Talla

Tattaunawar da aka yi tsakanin Girka da masu bin ta bashi, don neman mafita ga sabanin da ke tsakaninsu da aka shafe watanni biyar, ta kawo karshe ne ba tare da an cim ma matsaya ba.

Amma Shugaban Faransa Francois Hollande ya jaddada cewa za su yi iya kokarinsu domin shawo kan matsalar Girka da ke barazanar ficewa daga kasashen da ke amfnai da takardar kudin Yuro.

Tarayyar Turai Asususn lamuni na duniya IMF, sun kawar da yiwuwar kara wa hukumomin na Birnin Athens lokacin don samun damar biyan bashin da ke kan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.