Isa ga babban shafi
Kasashen Turai

Kasashen Turai sun kammala taro kan rikicin bashin Girka

Taron shugabannin Kasashen Turai kan batun rikicin bashin da ya dabaibaye kasar Girka, ya kawo karshe a cikin daren jiya a birnin Brussels, inda mahalartansa ke cewa an samu gagarumin ci gaba a kokarin da ake na cimma yarjejeniyar karshe kan yadda Girka za ta ci gaba da kasancewa a cikin kasashen masu amfani da takardar kudin Euro.

shugabannin Kasashen Turai
shugabannin Kasashen Turai REUTERS/Emmanuel Dunand/Pool
Talla

Bayan kammala taron shugabannin sun bukaci ministocinsu na kudi da sake gudanar da wata sabuwar tattaunawa a ranar laraba mai zuwa domin cimma matsaya kafin gagarumin taron da shuggabannin kasashen na Turai 28 za su gudanar a ranar Alhamis.

Shugaban hukumar nahiyar Turai, Jean Claude Juncker ya ce, ya gamsu cewa za su iya kawo karshen wannan matsala ta Girka da aka kwashe tsawon watanni 5 ana kokarin shawo kanta kuma ya bada tabbacin cimma matsaya ta karshe a cikin wannna makon, yayin da shima shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa ana dab da samar da yarjejeniyar karshe, to saida akwai sauran aiki a gabansu.

A nata bangaren kuwa, shugabar Gwamanatin Jamus Angela Markel ta gargadi cewa, ya kamata a kara kaimi a wannan lokacin yayin da ta yaba da tsare tsaren da Girka ta gabatar inda ta ce mataki ne da zai bada damar cigaba da tattaunawa dangane da tsamo Girka daga matsalar da ta tsinci kanta a ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.