Isa ga babban shafi
Faransa

An bukaci Faransa ta bada bayanai kan lalata da Kananan yara

Kungiyar kare hakkin kananan yara ta Save the Children ta bukaci gwamnatin Kasar Faransa da Majalisar Dinkin Duniya da su bada cikakkun bayanai game da zarge zargen da ake yiwa dakarun Faransa na yin lalata da kananan yara a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

A wata sanarwa data aikawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP, Kungiyar dake fafutukan kare hakkin kananan yara a fadin duniya ta ce, idan aka samu cikakkun hujjoji game da wannan batun, yana da matukar mukhimmaci a dau kwararan matakai akan wadanda aka samu da aikata laifin lalatan da Kananan yaran.

Kamar yadda wata majiyar shara’ar Kasar Faransa ta bayyana, dakarun soji 14 da aka tura domin aikin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun aikata laifin da ake zargin su da shi na lalata da kananan yara da ya hada da yan shekaru 9 kuma suna baran abincin da za su ci ne.

A nashi bangaren, Shugaban Kasar ta Faransa Francois Hollande ya lashi takobin hukunta sojin da aka tabbatar da aikata laifin, kuma ya yi alwashin ne, kwana daya da Jaridar Guardian ta Birtaniya ta fitar da labarin, bayan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.