Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

CAR: An zargi sojojin Faransa da yin lalata da yara

Gwamnatin Kasar Faransa ta kaddamar da bincike kan zargin lalata da kananan yara da ake yi wa sojojinta da ke aikin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ma’aikatar tsaron kasar tace hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar ce ta sanar da gwamnatin halin da ake ciki a karshen watan Yulin bara, abinda ya sa kasar ta fara bincike akai.

Sojojin Faransa na shirin shiga jirgi a Djamena kasar Chadi
Sojojin Faransa na shirin shiga jirgi a Djamena kasar Chadi REUTERS
Talla

Ma’aikatar tsaron Faransa ta sha alwashin daukar mataki akai idan har aka tabbatar da gaskiyar zargin.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya y ace Kimanin yara kanana 10 ne a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Sojojin suka yi lalata da su a kusa tashar jirgin sama a Bangui babban birnin kasar tsakanin watan Disemban 2010 zuwa Yunin 2014.

Tun a watan Disemban 2013 Faransa ta tura dakarunta zuwa kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya bayan kasar ta fada rikici mai nasaba da addini da kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.