Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Djotodia da Bozize sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Tsoffin shugabannin kasar Jamhuriyar Africa ta Tsakiya, Francois Bozize da Michel Djotodia sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kasar, inda rikicin kasar ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Tsoffin Shugabannin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Michel Djotodia da François Bozizé
Tsoffin Shugabannin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Michel Djotodia da François Bozizé AFP PHOTO / STEVE JORDAN
Talla

An kulla yarjejeniyar ne a birnin Nairobi na kasar Kenya, a sa idon shugaba Uhuru Kenyatta.

Duk da dai ba a bayyana hakikanin abin da ke kunshe cikin yarjejeniyar ba, amma tsohon shugaba Francois Bozize ya shaida wa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa yarjeniyar ba ta kunshin wata shadarar da ke bayar da dama ga tsofaffin shugabannin su yi takarar shugabancin kasar ba.

Ya ce an sami kiki-kaka a tattaunawar kan wannan lamarin.

Dama an dade ana zargin mutanen biyu da dawo da hannun agogo baya, a kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a kasar.

Sai dai Bozize ya ce shi a shirye ya ke a samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa.
A na shi bangaren tsohon shugaba Michel Djotodia ya ce wannan mai cike da tarihi, da zai taimaka a samar da mafita kan rikicin kasar Afrika ta Tsakiya.

Yarjejeniyar da aka kulla jiya Talata a birnin Nairobi, ta sami halartar shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, sai dai wakilan gwamnatin rikon kwaryar ba su sami halarta da birnin Bangui ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.