An saki Bafaransar da aka sace a Afrika ta tsakiya
Ministan Harakokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya tabbatar da cewa an saki Jami’ar agaji Bafaransa da Mayakan anti-balaka suka sace a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. Amma mahukuntan na Faransa ba su bayyana yadda aka saki Claudia Priest ba.
Wallafawa ranar:
A ranar Litinin ne aka sake Priest mai shekaru 67 tare da wani dan kasar Afrika ta tsakiya a birnin Bangui.
Ana danganta sace Jami’an agaji a matsayin martani da Mayakan balaka suka mayar bayan cafke wasu shugabanninsu a karshen makon da ya gabata.
Mayakan Balaka dai Kiristoci ne da ke fada da Mayakan Seleka Musulmi a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, tun bayan da Seleka ta karbe ikon gwamnati a watan Maris din 2013.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu