‘Yan ta’adda sun kashe ‘yan sanda 15 a Mexico
Hukumomin kasar Mexico sun ce wata kungiyar yan ta’adda ta kashe ‘Yan Sandan kasar 15 a wani kwantan baunar da suka yi musu a yammacin kasar
Wallafawa ranar:
Kwamishinan tsaron Jihar Jalisco, Francisco Alejandro Solorio, ya ce an tare tawagar ‘yan Sandan ne akan hanyar su ta zuwa Guadalajara, inda nan take aka kashe 15 daga cikinsu, yayin da 5 kuma suka samu munanan raunuka.
Kasar Mexico na fama da kungiyoyin masu hada-hadar kwayoyi da kuma safarar su zuwa kasashen waje.
Matsalar safarar miyagun kwayoyi dai matsala ce da ta zame wa gwamnatocin kasa-da-kasa alakakai, inda suke ci gaba da daukar matakan kamewa da kuma gurfanar da wadanda ake samu da laifin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu