Isa ga babban shafi
Mexico

An kama babban Kartagin ‘yan kwaya a Mexico

Hukumomi a kasar Mexico, sun bayyana kama babban Kartagin ‘yan Kungiyar Zeta, masu safarar miyagun kwayoyi Omar Trevino a yankin arewacin birnin Monterrey, sai dai kamun nashi na tada fargaban harzukar mambobin Dabarsa

dallasnews.com
Talla

Yanzu haka dai ana ci gaba da tsare babban Kartagin ne da aka fi sani da suna “Z-42” a Ofishin Soji da ‘yan sanda na yankin San Pedro Garza Garcia da ke a jihar Nuevo Leon kamar yadda was u jami’an gwamnati biyu suka bayyanawa Kamfanin dillancin labarai na AFP.

Trevino, mai shekaru 41, ya dare kan jagorancin kungiyar ‘yan Dabar Zeta masu safarar miyagun kwayoyi ne, bayan da aka yayansa Miguel Angel Trevino, ko “Z-40” da ake masa lakabi, a yankin Arewa maso gabashin jihar Tamaulipas cikin Watan Yulin shekarar 2013 da ta gabata.

Kamin kama shi dai hukumar tsaron kasar Amurka ta taba bada tayin biyan Dollar Miliyan 5 ga duk wanda ya bada cikakken bayani akan Omar Trevino, har aka kama shi, a yayinda takwararta ta kasar Mexico kuma, ta bada nata tayin na Dollar Miliyan 2.

Wannan kamen dai ga alama ya baiwa shugaban kasar ta Mexico Enrique Pena Nieto wata babar nasara akan yaki da gwamnatinsa ke yi da masu safarra miyagun kwayoyi, kuma ya zo ne a yayin da al’ummar kasar keta kokawa da yadda gwamnatin ke yiwa sha’anin tsaro rikon Sakainiyar Kashi.

Sai dai masu lura da al’amurra na cewar kamun, ba fa shi ne zai kai karshen matsalar safarra miyagun kwayoyi a cikin kasar ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.