Isa ga babban shafi
Colombia

Colombia za ta dakatar da kai hari ga ‘yan kungiyar FARC

Shugaban Kasar Colombia Juan Manuel Santos yace sojojin kasar zasu daina kai harin sama na wata guda kan ‘Yantawayen kungiyar FARC a yunkurin kawo karshen yakin basasa mafi tsayi a Yankin Amurka ta kudu

De izquierda a derecha, el representante de las FARC en las negociaciones de La Habana, Iván Márquez, el exsecretario general de la ONU, Kofi Annan, y el negociador del gobierno colombiano, Humberto de la Calle, La Habana, 27 de febrero de 2015.
De izquierda a derecha, el representante de las FARC en las negociaciones de La Habana, Iván Márquez, el exsecretario general de la ONU, Kofi Annan, y el negociador del gobierno colombiano, Humberto de la Calle, La Habana, 27 de febrero de 2015. REUTERS
Talla

A sanarwar da ya yi ta kafar Talabijin, shugaban ya ce ya umurci Ministan tsaron kasar da kwamandojin soji da su daina kai harin sama kan sansanin ‘yantawayen, har sai idan ‘yantawayen sun ci gaba da yiwa kasar barazana.

Akalla mutane 220,000 ne aka kashe a yakin da Dakarun kasar ta Colombia ke yi da ‘yan tawayen FARC masu dauke da muggan makamai.

Santos ya ce akwai alamun da ke nuna cewar a wannan karon kungiyar FARC na nuna goyon bayan shirin gwamnati, na sasantawa a tsakaninsu da kuma samar da zaman lafiya.

Sai dai ya yi kashedin cewar muddin suka hangi wata barazana, to za su komawa aniyarsu ta sauke Tabaren Wuta a yankunan da ‘yantawaye suke fakewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.