Isa ga babban shafi
Jamus

An kwashe mutane 10,000 akan fargaban tashin Bam a Jamus

Hukumomi a kasar Jamus sun kwashe mutane akalla dubu 10 a wasu yankuna da ke kusada tashar Jirgin kasa ta Potsdam, sakamakon gano wani abinda ake zaton Bam ne aka dasa

flickrhivemind.net
Talla

An ce dai da ganin curin abin, nan-da-nan jami’an tsaro suka killace wurin, aka kuma hana kowa wucewa ta yankin. Sai dai kuma daga baya an gano cewa irin Bamabaman da aka dasa ne tun lokacin yakin Duniya na farko a shekara ta 1945.

Hukumomin kasar sun ce akwai ire-iren Bamabaman wancan lokaci akalla 3,000 da aka daddasa a yankin tun, shekaru kusan 60 da suka gabata.

Wannan al’amarin dai ya tada hankulan mutane ba kadan ba lura da yadda yanzu kasashen Turai ke fuskantar bulluwar mayakan jihadi da kan yi tafiyayyiya zuwa kassahen Siriya da Iraqi, domin taimakawa mayakan ISIL fada da Dakarun hadin guiwa na kasashen Duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.