Isa ga babban shafi
Ebola

Tarayyar Turai ta kara bayar da tallafin yakar Ebola

Kungiyar Kasashen Turai ta sanar da wani shirin bai wa Afrika ta Yamma Karin tallafin kudi na euro miliyan 61 don yaki da cutar ebola. Tallafin kuma ya shafi bayar da horo ga likitoci da Jami’an da ke aikin kawar da Ebola a kasashen yammacin Afrika.

Tiken Jah Fakoly yana rike da sakon yaki da Ebola a Afrika
Tiken Jah Fakoly yana rike da sakon yaki da Ebola a Afrika RFI/ Stefanie Otto
Talla

Neven Mimica, kwamishiniyar kula da hadin kai da ci gaba ta sanar da tallafin ne lokacin da ta kai ziyarar aiki kasar Guinea, daga cikin kasashen da ke fama da matsalar cutar.

Mimica tace kungiyar kasashen Turai na jin zafin halin da al’ummar kasar Guinea suka samu kansu a ciki.

Cutar Ebola ta yi sanadin mutuwar mutane 6,300 a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo, yayin da a Guinea kawai mutane 1,400 suka mutu.

Yanzu haka kuma an bayyana cewa Saliyo ce ke da yawan mutanen da ke dauke da cutar fiye da Liberia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.