Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU tana bukatar likitoci 5,000 don yaki da Ebola

Kungiyar Tarrayar Turai ta yi kira ga mambobin kasashenta akan bukatar tura likitoci akalla dubu biyar zuwa kasashen yammancin Afrika masu fama da annobar cutar Ebola domin dakile yaduwar cutar da ta zama alakakai a yankin.

Barbara Kanam.
Barbara Kanam. RFI/ Stefanie Otto
Talla

Manyan jami’an kungiyar Tarrayar Turai sun sanar da cewa suna ganawa da gwamnatoci daga kasashen Nahiyar domin samun goyon bayansu wajen samun nasarar yakar cutar Ebola.

Jami’an sun bukaci taimakon likitoci da dama da ma’aikatan kiwon lafiya da ke da niyyar yin aikin sa-kai a kasashen Liberia da Guinea da Saliyo inda cutar tafi kamari.

Kungiyar Tarrayar Turai dai ta sami tallafin kudi da ya kai akalla Euro Biliyan daya sai dai kungiyar tace tana bukatar Karin likitoci akalla dubu biyar da za su taimaka wajen hana yaduwar cutar ta Ebola a yammancin Afrika.

Cutar da ta fi bulla a wannan shekarar shekarar ta kama mutane sama da dubu goma sha biyar tare da hallaka dubu biyar da dari biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.