Isa ga babban shafi
Ebola

Ana lura da lafiyar mutane 600 a Mali

Hukumomin Kasar Mali sun ce suna lura da lafiyar mutane kusan 600 saboda mu’amalar da suka yi da wadanda suka kamu da cutar Ebola a cikin kasar. Mali ta dauki matakan ne domin dakile bazuwar Ebola da ke kisan Jama’a a cikin hanzari.

Jami'an kiwon lafiya suna aikin daukar matakan kariya domin kaucewa yaduwar cutar Ebola a Mali
Jami'an kiwon lafiya suna aikin daukar matakan kariya domin kaucewa yaduwar cutar Ebola a Mali REUTERS/Joe Penney
Talla

Samba Sow na kungiyar agajin gaggawa kan yaki da cutar Ebola a Bamako ya ce jami’an sa na ci gaba da sa ido a kauyen Kouremale da ke iyakan kasar Guinea.

Jami’an lafiyar Mali sun gudanar da wani taro inda suka dauki matakin kara tsaro akan iyakokin kasar.

Mali na daukar sabbin matakan ne bayan mutuwar wani Malamin Guinea da wata Jami’ar Lafiya da ta hidima da shi a Bamako.

A watan Oktoba ne wata karamar Yarinya ta shigo da Ebola a Mali daga Guinea, kuma yanzu mutane uku suka mutu sakamakon bullar Ebola a Mali.

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya bukaci mutanen Mali su dauki matakan kariya, musamman a kauyen Kouremale da ke kusa da Guinea inda Ebola ta kashe Mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.