Isa ga babban shafi
Mali

Yarinyar da ta shigo da Ebola a Mali ta mutu

Mahukuntan Mali na kokarin kwantar da hankalin mutanen kasar game da cutar Ebola bayan mutuwar wata karamar Yarinya da ta shigo da cutar daga Guinea. Wannan ne karo na farko da aka samu bullar cutar Ebola a Mali.

Ana horar da ma'aikatan sa-kai akan yadda zasu yi aikin kula da majinyatan Ebola a Asibitin Henri MondorCreteil
Ana horar da ma'aikatan sa-kai akan yadda zasu yi aikin kula da majinyatan Ebola a Asibitin Henri MondorCreteil Reuters/Philippe Wojazer
Talla

Kimanin mutane 4,922 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.

Shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita ya shaidawa Radiyon Faransa cewa gwamnatinsa tana kokarin kwantar da hankalin ‘Yan kasa tare da daukar matakan da suka dace domin dakile bazuwar cutar.

Karamar Yarinyar ta shigo Mali ne daga Guinea tare da kakarta a motar kasuwa, kuma tun a cikin motar ciwon na Ebola ya tsananta.

Yanzu haka mahukuntan Mali sun ce suna lura da lafiyar mutane 43 da suka yi mu’amula da karamar yarinyar da Kakarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.