Isa ga babban shafi
Mali

Ebola: Ana lura da lafiyar mutane da dama a Mali

Kimanin mutane 43 ne ake lura da lafiyarsu a Mali wadanda suka yi mu’amula da Yarinya ‘Yar shekaru biyu da ta yi sanadin bullar cutar Ebola a cikin kasar daga Guinea. Wannan ne karo na farko Ebola ta bulla a kasar Mali. Kuma Jami’an kiwon lafiya suna lura da lafiyar mutane 43 da suka yi mu’amula da Yarinyar.

Cutar Ebola a kasar Mali
Cutar Ebola a kasar Mali
Talla

Goma daga cikin mutanen da ake lura da lafiyarsu Jami’an kiwon lafiya ne, cikinsu kuma akwai wadanda suka yi hidima da yarinyar mai dauke da Ebola.

A ranar Alhamis ne Ministan Lafiya na kasar Mali ya tabbatar da bullar Ebola a Mali bayan tabbatar da gwaji akan karamar Yarinyar.

Mutane kusan 5,000 suka mutu a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo saboda Ebola, kuma masana yanzu sun bayyana fargaba akan barazanar yaduwar Cutar Ebola a kasashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.