Kasashen Duniya na shirin daukar tsauraran matakai a kan cutar Ebola
Shugabannin kasashen Birtaniya, Amurka, Faransa, Jamus da kuma Italiya, sun bayyana cewa Ebola na a matsayin annoba mafi muni da duniya ta taba fuskanta a cikin shekarun baya bayan nan.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hakkan dai na zuwa ne bayan wata sanarwa da fadar firaministan Birtaniya david Cameron ta fitar bayan da shugaba Barack Obama ya zanta da shugabannin kasashen ta wayar talho, ta bayyana cewa dole ne duniya ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin tunkarar wannan annoba da kawo yanzu ta kashe sama da mutane dubu 4.
A dai bangaren hukumar gudanar da jami’o’in a wasu jihohin kasar Amurka sun soma nuna wa daliban kasashen da ke fama da cutar Ebola wariya, lamarin da kuma ya soma tayar da hankulan wasu daga cikin daliban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu