Isa ga babban shafi
Ebola

An samu raguwar bazuwar Ebola a Liberia

Kungiyar likitocin bayar da agaji ta duniya Medicine Sans Frontiers ta bayyana samun raguwar yawan masu kamuwa da cutar Ebola a kasar Liberia, musamman a Monrovia babban birnin kasar, inda kungiyar tace duk da haka sai an kara zage dantse wajen yaki da cutar.

Jami'an kiwon lafiya da ke aikin kawar da cutar Ebola à Monrovia, kasar Liberia
Jami'an kiwon lafiya da ke aikin kawar da cutar Ebola à Monrovia, kasar Liberia REUTERS/James Giahyue
Talla

Dr Bernadette ta kungiyar ta bayyana haka tana mai cewa wannan wani ci gaba ne mai karfafa guiwa dangane da yaki da annobar Ebola.

Likitocin sun ce suna ci gaba da iya kokarinsu wajen dakile bazuwar cutar da ta kashe mutane da dama a Liberia.

, haka kuma bamu rage yawan ma’aikatamu ba, domin ya zama wajibi a cigaba da kokari, domin bamu san me zai iya faruwa a cikin makwanni masu zuwa ba,

MSF tace tana ci gaba da aiki a cikin karkara wajen wayar da kan jama’a tare da aiki da su wajen gano wadanda suka kamu domin tallafa wa iyalansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.