Isa ga babban shafi
Ebola

Likitocin Najeriya 250 sun tafi yaki da Ebola

Kungiyar Kasashen Afrika ta AU ta sanar da tura jami’an kula da lafiya 250 daga Najeriya zuwa kasashen da ke fama da Ebola, Liberia da Saliyo da Guinea domin yaki da cutar. Nan gaba ana sa ran wasu likitocin daga wasu kasashe za su shiga aikin agajin na yakar cutar da ta lakume rayukan dubban mutane a yammacin Afrika.

Jami'an lafiya suna aikin kawar da Ebola a Monrovia kasar Liberia
Jami'an lafiya suna aikin kawar da Ebola a Monrovia kasar Liberia John Moore/Getty Images
Talla

Shugabar gudanarwar kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma ce ta bayyana haka lokacin da ta ke rokon kamfanonin jiragen sama da su koma aikin sufuri zuwa kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.

Shugabar kuma ta yi kira ga kamfanonin sadarwa su dauki nauyin tallafawa aikin yaki da Ebola, kamar yadda kamfanin MTN da Dangote suka da tallafin kudi.

A Najeriya an yi nasarar kawar da Ebola a watan Oktoba bayan wani mutumin Liberia ya shigo da cutar a Lagos inda ta yi sanadin mutuwar mutane 8

Hukumar lafitya ta WHO tace adadin mutane 6,070 ne Ebola ta kashe, mafi yawanci a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.