Isa ga babban shafi
Fransa

Jadawalin bukukuwan ranar kwato Faransa daga 'yan Nazi

Fadar shugaban kasar Faransa, ta bayyana yadda za a gudanar bukukuwan cika shekaru 70 da sojojin kawance suka kwato kasar daga hannun dakarun Hitler a lokacin yakin duniya na biyu.

Talla

Za a dai gudanar da wadannan bukukuwa ne a ranar 6 ga watan Yuni mai zuwa a karkashin jagorancin shugaba Francois Hollande.

A jimilce dai shugabannin kasashen duniya 18 ne suka bayyana aniyarsu ta halartar wadannan bukukuwa da za a gudanar a gabar ruwan Normandie, wato yankin da sojojin kawance suka fara dira na zumma fatattakar sojojin Nazi a shekarar 1944.

Daga cikin shugabannin kuwa har da Barack Obama na Amurka, da Vladamir Poutine na kasar Rasha, da Firaministan Canada Stephen Harper. Har ila yau akwai waziyar kasar Jamus Angela Merkel da sarauniyar Ingila Elisabeth ta biyu da kuma sarki Philippes na kasar Belgium.

A jimilce dai mutane sama da dubu7 ne za su halarci wadannan bukukuwa cikinsu kuwa har da tsoffin sojoji 900, kuma 800 daga cikinsu za su fito ne daga kasashen ketare.

An tanadi makada bajudala har guda 650, domin kadawa sojojin da za su yi fareti, kunma daga nan ne shugaba Hollande da takwaransa na Amurka Barack Obama za su ziyarci makabartar Colle-Ville-Sur-Mer domin ajiye furanni akan kaburburan tsoffin sojoji dubu 10 da suka kwanta dama a lokacin yakin duniya na biyu cikin su kuwa har da wani da aka ce kanin tsohon shugaban Amurka Roosevetl ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.