Isa ga babban shafi
Faransa

Mai ba Hollande shawara ya yi murabus

Mai bai wa shugaban Faransa Francois Hollande shawara ya ajiye mukaminsa a yau Juma’a bayan zarginsa da yin fatali da kudade wajen tafiyar da rayuwarsa. Wannan dai ana ganin wata baraka ce ta kunno kai ga gwamnatin Hollande.

Aquilino Morelle, mai ba Shugaban Faransa shawara
Aquilino Morelle, mai ba Shugaban Faransa shawara AFP PHOTO / FRED DUFOUR
Talla

Aquilino Morelle ya bayyana yin murabus ne a cikin wata sanarwa tare da yin watsi da zargin da ake masa na yin fatali da kudade wajen tafiyar shagalin rayuwarsa.

A cikin sanarwar, mai ba shugaban shawara yace ya yi murabus ne don kare mutuncinsa.

Tun lokacin da aka kaddamar da bincike akan Mista morelle ya ke fuskantar kalubale wajen tafiyar da ayyukansa.

Akwai kuma zargi da ake masa akan ya keta dokar aiki a Faransa saboda mu’amula da ya yi da wani kamfani samar magani a shekarar 2007 a lokacin yana babban Jami’I a hukumar kula da jin dadin jama’a.

Amma babban zargin da ake masa shi ne yin almubbazzaranci da kudade a dai dai lokacin da gwamnati ke aiwatar da matakan tuke bakin aljihun gwamnati domin cim ma bukatar turai na datse kasafin kudin kasar.

Wata majiya daga fadar Hollande tace duk bayan wata biyu Morlle yana yin oadar sabbin takalmi kusan 30, zargin da kuma be ce komi akai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.