Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyyar Le Pen ta bayar da mamaki a Faransa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai sake wani salon siyasa a gwamnatinsa bayan Jam’iyyarsa ta gurguzu ta sha kashi a zaben kananan hukumomi da aka gudanar zagaye na biyu inda Jam’iyyar adawa ta ‘Yan kishin kasa ta lashe birane 11.

Katin Zaben kananan hukumomi a Faransa
Katin Zaben kananan hukumomi a Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Jam’iyyar National Front ta Marine Le Pen tana kan hanyar lashe kujerun Kansiloli da dama, wanda shi ne sakamako mafi kyau da Jam’iyyar ta samu a tarihin siyasar Faransa.

Haka kuma Jam’iyyar UMP mai adawa ta tsohon shugaban kasa Nicolkas Sarkozy ta samu nasarar lashe wasu manyan biranen Faransa da suka hada da Limoges da Toulouse da Saint Etienne. Amma Jam’iyyar gurguzu ta shugaba Hollande ce ta lashe kujerar magajin garin birnin Paris.

Zaben zagaye na biyu da aka gudanar a ranar lahadi bai samu karbuwa ba sosai ida aka bayyana cewa kashi 20 ne cikin 100 kacal na masu zabe suka kada kuri’a idan aka auna da zaben shekara ta 2008 inda aka samu kashi 23.68 na masu zabe.

Zaben ya shafi kananan hukumomi 6, 455 mafi yawancinsu a manyan birane.

Wannan dai ba karamin koma baya ba ne da kuma kalubale ga shugaban kasar na jam’iyar gurguzu Francois Hollande wanda gwamnatinsa ake ganin a duk jikinta mabuga ne daga ‘yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.