Isa ga babban shafi
Faransa

Mayakan Jihadi sun yi wa Faransa barazana

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yace Faransa ta dauki matakan tsaro bayan wani sakon kisan shi da mayakan Jihadi suka aiko a cikin wata sanarwa a shafin Intanet domin daukar fansa akan rikicin kasar Mali da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Faransa ta aika da dakarunta domin aikin wanzar da zaman lafiya.

Shugaba Francois Hollande yana ganawa da Sojojin Faransa a birnin Bangui na kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Shugaba Francois Hollande yana ganawa da Sojojin Faransa a birnin Bangui na kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya REUTERS/Sia Kambou
Talla

Shugaba Hollande yace sun dade suna fuskantar irin wannan barazana domin ba wannan ne karon farko ba.

Barazanar ta fito ne daga shafin wata Kungiyar Mayaka mai suna Minbar Jihadi Network da aka bayyana tana da alaka da Kungiyar Al Qaeda.

Wata majiya a fadar shugaban kasar Faransa tace duk da cewa gwamnatin kasar na sa ido amma sun dade suna samun irin wannan sakon na barazana.

A cikin Sanarwar da makusantan na Kungiyar Alka’ida suka aiko a shafin Intanet, kungiyar ta bukaci mambobinta da ke Faransa su kashe Shugaba Hollande tare da azabtar da gwamnatinsa, ta hanyar cusa masu bakin cikin da har sai sun gwammace mutuwa da rayuwa.

Mayakan sun ce Hollande da dakarunsa ba za su taba samun kwanciyar hankali ba a kasar Faransa kamar yadda musulmin kasar Mali da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ke cikin irin wannan hali a kasashensu.

Kasar Faransa ta aika da dakaru kusan guda 2,000 a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya domin aikin wanzar da zaman lafiya a rikicin kasar day a rikide daga siyasa ta koma na addini. A bara ne kuma Faransa ta kwato arewacin Mali daga hannun mayakan da suka karbe ikon yankin a lokacin da Sojoji suka kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.