Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Kosovo ta amince da kafa kotun hukunta laifufukan yaki

Majalisar Dokokin Kosovo ta amince da kafa kotun kasa da kasa, wace za ta yi shara’ar hukumta laifukan yaki, da ake zargin mayakan kungiyar yan awaren yankin Kosovo UCK da aikata a lokacin yakin basasar Sabiya da kosovo na (1998-99).

Kotun Manyan laifuka a Kosovo
Kotun Manyan laifuka a Kosovo www.balcanicaucaso.org
Talla

Dokar kafa kotun wace ta samu amincewar yan majalisu 89 daga cikin su 120. 22 daga cikinsu sun nuna rashin amincewarsu da ita a yayinda 2 suka kauracewa zaben

Kafin kada kuri’ar dai PM Kosovo Hashim Thaçi ya shaidawa yan majalisar dokokin cewa, kafa wannan kotu shine zai wanke sunan Kosovo da ya bace, sakamakon zargi marar tushe da rahoton Marty ya yi mata.

Rahotun kungiyar tarayyar turai dai, kan rikicin yankin na Kosovo da Dick Marty ya rubuta, ya zargi mayakan kungiyar yan awaren yankin Kosovo daga Saviya (UCK) da aikata laifukan yaki tare da cin zarafin bil’adama a lokacin yakin na Savia da Kosovo
Har ila yau rahoton ya tabo zargin safarar sassan jikin dan adam na fursunonin saviyawa da Roms su 500, a lokacin yakin, wanda yace mayakan yan awaren na Kosovo suka aikata, karkashin jagorancin shugabansu da ya kasance shi da kansa PM. Thaçi, zargin da ya karyata

Yakin Kosovo dai wanda ya balle a 1998 zuwa 99 yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 13.000 mafi yawancinsu kuma Albaniyawan Kosovo ne, kafin kawo karshensa da hare haren jiragen saman da kungiyar tsaro ta Nato kan Sabiya, wanda hakan ya tilastawa saviyan ta kawo karshen muzgunawa da cin zarafin mayakan yan awaren yankin na kosovo da kuma fararen hula albaniyawa

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.