Isa ga babban shafi
Spain

Spain ta kekasa kasa dangane da ‘yancin kan Kosovo

Spain ta fada juma’ar nan cewa ita fa har yanzu ba zata amince da cin gashin kan Kosovo ba, duk da cewa kotun duniya ta yanke hukunci kan halaccin ballerwar da ta yi daga Servia.Mataimakiyar Firayi minister kasar Maria Teresa ta shaida wa taron manema labarai cewa “har yanzu muna nan kan bakanmu, ba zamu amince da cin gashin kan Kosovo ba, kuma zamu ci gaba da yin kiran zaman tattaunawa don cim ma yarjejeniya tsakanin bangarorin da abin ya shafa.Spain wadda ita ma tana fuskantar matsin lambar wadanda ke son ballewa a yankunan Catalonia da Basque, ta ki bin sahun akasarin kawayenta na tarayyar turai, inda ta ki amincewa da ‘yancin gashin kan Kosovo. 

María Teresa Mataimakiyar Firayi Ministan Spain
María Teresa Mataimakiyar Firayi Ministan Spain Foto: J.Batallé/RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.