Isa ga babban shafi
Ukraine

Tymoshenko zata yi takara a zaben Ukraine

Daya daga cikin shahrarrun ‘yan siyasar kasar Ukraine, kuma tsohuwar Firaministan kasar Yulia Tymoshenko, ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar neman mukamin shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a nan gaba, domin maye gurbin Victor Yanukovich, da ka bar mukamin shi a kwanakin baya.Yulia Tymoshenko macen farko da ta rike mukamin Firaminista a kasar Ukraine, na da shekaru 53 a duniya, a jiya alhamis ne ta sanar da manema labarai cewa za ta tsaya takarar shugabancin kasar da za'a gudanar a ranar 25 ga watan mayu mai zuwa.Tymoshenko na daya daga cikin ‘yan siyasar kasar ta Ukraine da ke da kwarjini da kwazo da kuma rashin tsoro da ta jagoranci gwagwarmayar da aka yi a shekara ta 2004 domin samar da sauyi a kasar, to sai dai duk da haka ta fadi a zaben da ya bawa shugaba Yanukovich nasara a shekara ta 2010.bayan wannan nasarar ce yanukovich ya sa Tymoshenko gaba wajen tuhumar ta da laifin yin almundahana da kudin kasa ta hanyar amfani da matsayinta, zargin da ya kai ga hukunci dauri har na tsawon shekaru 7 a gidan yari.Sai dai kuma Tymoshenko ta fito daga gidan yari a daidai lokacin da take jinya kan gadon asibiti a cikin watan Febrairun da ya gabata, bayan Yanukovich ya rasa mukaminsa bisa zargin kashe mutane dari daya da ke zanga zangar adawa da gwamnatinsa.Yulia Tymoshenko ta sha alwashin kawo karshen tazarar da ke tsakanin masu kudin kasar, da gwamnati da ta ce suna azurta kansu da kansu.  

Tsohuwar Friministan Ukraine, Yulia Tymoshenko
Tsohuwar Friministan Ukraine, Yulia Tymoshenko
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.