Isa ga babban shafi
Ukraine

Kotun Ukraine ta yi watsi da bukatar Tymoshenko

Kotun kasar Ukraine ta yi watsi da daukaka kara da tsohuwar shugabar adawar kasar ta shigar Yulia Tymoshenko domin neman a sassauta hukuncin daurin da ake mata bayan shafe sama da watanni biyu ‘Yan adawa suna zanga-zangar nuna goyon bayan ganin an sake ta.

Shugabannin Adawa a kasar Ukraine suna sanye da raga mai dauke da hoton Yulia Tymoshenko
Shugabannin Adawa a kasar Ukraine suna sanye da raga mai dauke da hoton Yulia Tymoshenko REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Lauyan da ke kare Tsohuwar Firaministar, shi ne ya shigar da bukatar inda a cikin sassaucin ya ke neman a ba Yulia Tymoshenko damar yin amfani da wayar Salula tare da ba ta damar yin yawo a cikin gari da kuma karin yawan adadin mutanen da ke kawo ma ta ziyara.

Daruruwan mutane ne dai suka mamaye harabar kotun masu ganin neman an saki Tsohuwar Firaministar duk da Tymoshenko ta kauracewa zaman Kotun.

A shekarar 2011 ne aka yanke wa Yulia Tymoshenko hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari akan laifin cin mutuncin kujerarta ta Firaminista, amma an kwashe tsawon shekaru tana jinya a gadon asibitin Gidan yari saboda rashin lafiyar baya da ta ke fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.