Isa ga babban shafi
Rasha-EU-Ukraine

Crimea: Kungiyar Turai ta kakabawa ‘Yan Rasha da Ukraine 21 takunkumi

Kungiyar kasashen Turai ta kakabawa wasu mutanen Rasha da Ukraine Takunkumin tafiye tafiye da rufe asusun ajiyarsu a Turai wadanda aka zarga sun taka rawa ga zaben jin ra’ayin jama’a da mutanen yankin Crimea suka amince su koma ikon Tarayyar Rasha.

Wani Sojan sa-kai rike da tutar Rasha a kan iyaka tsakanin Simferofol da Savastopol a yankin Crimea
Wani Sojan sa-kai rike da tutar Rasha a kan iyaka tsakanin Simferofol da Savastopol a yankin Crimea (©Reuters)
Talla

Tuni Rasha ta bayyana amincewa da mutanen Crimea amma kasashen Turai sun dauki matakin takunkumi ne bayan sun yi watsi da sakamakon zaben.

A ranar Lahadi ne mutanen Crimea suka amince su koma ikon Rasha sabanin Ukraine da gagarumn rinjaye kashi 97.

Kungiyar Turai ta lankayawa wasu mutanen Rasha da Ukraine 21 takunkumin ne ba tare da bayyana sunayensu ba.

Tun a watan Fabrairu ne sojojin sa-kai masu ra’ayin Rasha suka karbe ikon Crimea, lamarin da ya sa Amurka da kasashen Yammaci ke caccakar Rasha.

Matakin ballewar yankin Crimea ya bijiro ne tun lokacin da ‘Yan adawa masu ra’ayin Turai suka hambarar da gwamnatin Viktor Yanukovich mai ra’ayin Rasha a ranar 22 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.