Isa ga babban shafi
Faransa

Sufuri kyauta a Paris domin rage gurbatar yanayi

Hukumomin birnin Paris sun bayar da sanarwar barin ababan hawa su yi aiki kyauta tsawon kwanaki uku, don ba jama’a kwarin gwiwar barin motocinsu a gida, a wani mataki na magance matsalar gurbatar yanayi.

Gurbatar Yanayi a Birnin Paris
Gurbatar Yanayi a Birnin Paris REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Har yanzu kwararru na ci gaba da bayyana fargabar gurbatar iska a wasu yankunan Nahiyar Turai, lamarin da aka bayyana zai fi zafafa a kasar Faransa.

An shafe kwanaki ana gargadin jama’a kan yuwuwar samun wannan gurbacewar iska sakamakon alamun kurar a birnin Paris, da wasu biranen kasar Faransa.

Jagorantar kungiyar da ke kula da harkokin sufuri a birnin Paris da Jean-Paul Huchon, yace daga yau Juma’a da safe, za a ci gaba da safarar mutane masu ficewa daga birnin a kyauta, har zuwa yammacin ranar Lahadi.

Huchun yace an dauki wannan matakin ne, saboda kurar na iya barazana ga lafiyar mazauna birnin.

Masana kiwon lafiya sun ce Kurar na iya shiga cikin huhun bil Adama, tare da yin sanadiyyar kamuwa da cutar Asthma, da sauran cutukan da ke da alaka da numfashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.