Isa ga babban shafi
Faransa

Farkar Hollande ta nemi a biya ta diya

Masu shigar da kara a Faransa sun ce ana kan gudanar da binciken shari’a kan hotunan da wata mujalla ta buga dangane da rayuwar shugaba Francois Hollande da kuma farkarsa mai fitowa a cikin shirin Fim Julie Gayet.

Shugaban Faransa, François Hollande da hoton Farkarsa Julie Gayet
Shugaban Faransa, François Hollande da hoton Farkarsa Julie Gayet Reuters
Talla

Matukar dai aka gabatar da wannan batu a gaban kotu sannan kuma aka samu mujallar da laifin yin tonon silili kan al’amurran da suka shafi rayuwar Hollande da Gayet, ana iya cin mujallar tara ta euro Dubu 45 ko daurin shekaru daya a gidan yari.

Julie Gayet tana fitowa a cikin shirin Fim kuma mujallar ta nuna hotunanta a lokacin da ta ke isa a wani gidan shugaba Hollande na musamman.

A watan jiya ne da aka yayata mu’amular Hollande da Gayet, lamarin da har ya sa shugaban ya rabu da mudurwarsa da suka dade tare Valerie Trierweiler.

Akwai kudi euro 50,000 da Gayet ta nema mujallar da ta yada hutunanta ta biya ta diyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.