Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande zai dauki matakai akan matsalolin rayuwarsa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yace a shirye ya ke ya tunkari barakar da ta kunno kai a rayuwarsa game da alakar shi da wata mai shirin Fim Julie Gayet, bayan shugaban ya kaucewa tambayoyi akan makomar abokiyar zamansa Valerie Trierweiler a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.

Shugaban Faransa, François Hollande.
Shugaban Faransa, François Hollande. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Hollande ya amsa cewa suna fuskantar matsala tsakanin shi da Valerie Trierweiler bayan zargin yana mu’amula da ‘Yar Fim mai shekaru 41.

Shugaban yace zai bayar da haske akan huldar shi da Julie Gayet kafin ziyarar da zai kai a kasar Amurka a watan gobe.

Tuni aka gayyaci Trierweiler domin raka shugaban zuwa Fadar White House amma yanzu haka tana kwance a gadon asibiti saboda kaduwar da ta yi bayan jin labarin Hollande yana mu’amula da ‘Yar Fim.

An tambayi Hollande ko har yanzu Trierweiler ita ce First Lady amma shugaban ya kada baki yace yana fuskantar kalubale a rayuwar shi tare da kaucewa amsar tambayar da ya kira sirrin rayuwar shi.

Tun lokacin da wata Mujalla ta yada labarin Hollande yana mu’amula da ‘Yar Fim, aka kwashi Trierweiler mai shekaru 48 zuwa Asibiti.

Mujalar ta nuna hutunan Hollande da dama tare da Gayet a harabar wani gida da ke kusa da fadar shugaban kasa.

A hukumance dai wannan taron na manema labarai da shugaban Hollande ke shirin gabatarwa a tsakiyar ranar yau, an tsara shi ne da nufin bayyana irin rawar da gwamnatinsa ke taka domin farafado da tattalin arzikin kasar da kuma kirkiro da sabbin gurabobin ayyukan yi ga jama’a, amma bullar wannan batu na alaka tsakaninsa da Julie Gayet, shi ne ya karkatar da alkiblar haduwarsa da manema labarai.

Tuni dai shugaban babbar jam’iyyar adawa ta kasar Jean-Francois Cope ya bayyana lamarin a matsayin wanda zai iya dushe tauraruwar shugaba Hollande, yayin da David Assouline mai magana da yawun jam’iyyar gurguzu da ke kan karagar mulki, ke bayyana lamarin a matsayin wanda ya shafi rayuwar shugaban ta kashin kansa amma ba lamurransa na siyasa ba.

A cikin jawabin Shugaba Hollande ya dauki wasu sabbin alkawulla na sake dawowa da kasar a layin masu karfin tattalin arziki a Duniya, tare da samar da makomar da ta dace ga kamfanonin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.