Isa ga babban shafi
Faransa

An yi zanga-zangar adawa da manufofin Hollande a Faransa

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga zanga a birnin Paris da ke kasar Faransa, don nuna fushinsu ga manufofin shugaban kasa Francois Hollande, musamman halatta auran jinsi guda da aka yi a zamaninsa.

Masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Hollande a Faransa
Masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Hollande a Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Zanga-zangar da wasu kananan kungiyoyi suka kira tare da ‘Yan adawar kasar na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban kasar, Francois Hollande ke fuskantar kalubalen rabuwa da abokiyar zamansa.

Masu shirya taron sun ce akalla mutane 120,000 suka shiga zanga zangar da aka gudanar da ita a cikin ruwan sama, abinda ‘yan sanda suka musanta inda suke ce mutane 17,000 kawai suka shiga zanga-zangar.

Masu zanga zanga sun kuma bukaci janye dokar auran jinsi guda, yayin da wasu suka bukaci ficewa daga kungiyar kasashen Turai da kuma mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, lura da yadda aka hana wani mai shirin wasan kwaikwayo gudanar da wasansa.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun yi Allah waddai da abin fallasar da ya shafi shugaba Hollande da abokiyar zamansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.