Isa ga babban shafi
EU

An cim ma yarjejeniyar Banki a Kungiyar Turai

Kafin gudanar da taron shugabannin kasashen Tuai a birnin Brussels, Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da wata yarjejeniyar samar da kawancen banki tsakanin kasashen Nahiyar, domin magance matsalar tattalin arziki da ke addabarsu.

François Hollande na Faransa tare da Angela Merkel ta Jamus
François Hollande na Faransa tare da Angela Merkel ta Jamus REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Amma Yarjejeniyar da aka cim ma dole sai shugabannin kasashen na EU sun amince da ita kafin ta fara aiki.

Wannan yarjejeniyar wata dama ce da zata karfafa wa Angela Merkel da François Hollande kwarin gwiwa a kokarin da suke na inganta tattalin arzikin Turai.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tace ala tilas yanzu Kungiyar Tarayyar Turai ta bude sabbin shafin bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen da ke cikin Kungiyar.

Merkel ta fadi haka ne kwana daya bayan ta karbi rantsuwar fara wa’adi na uku a matsayin Shugabar Gwamnatin Jamus.

Angela Merkel tana da ra’ayin na kasashen Turai su yi aiki tare domin daidaita harkokin kudade da tattalin arzikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.