Isa ga babban shafi
Jamus

Markel ta bukaci Kwamitin sulhu na MDD da ya tallafawa ‘yan gudun hijirar Siriya

Shugabar Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel ta nemi Komitin Sulhu na Majalisar dunkin Duniya da ya kara ba da himma wajen tallafawa’yan gudun hijira na kasar Siriya, wadanda yakin kasar ya daidai ta.

La chancelière Angela Merkel a défendu  devant les députés allemands un projet économique mettant la justice sociale au coeur de ses priorités. Berlin, le 29 janvier 2014.
La chancelière Angela Merkel a défendu devant les députés allemands un projet économique mettant la justice sociale au coeur de ses priorités. Berlin, le 29 janvier 2014. REUTERS/Tobias Schwarz
Talla

Uwar Gida Angela Merkel na Magana ne bayan ta tattauna da PM kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan wanda yake ziyara a Jamus.

Merkel ta fadi cewa tattaunawa da kasashen Rusha, da China da ma kasar Iran cewar ya zama jazamun, domin a taimakawa bayin Allah da suka shiga mawuyacin hali sakamakon fadan Siriya da aka kwashe Shekaru 3 ana fafatawa.

Tace tattaunawan sulhu da akayi a Geneva makon jiya bai tsinana komi ba, ta fannin agazawa ‘yan gudun hijira, saboda haka ba wai za’a nade Hannu ne a zura Idanu al’amarin na kara munana kullum ba.

Amma abin bukata shine a tattauna da Rasha da China da kuma kasar Iran don su kawo tasu hanya.

Firaiministan Turkiyya Recef Tayyef Erdogan wanda yake ziyarar wannan kasa da keda mutane sama da miliyan 3 a ciki ya nemi a yi wasu sauye-sauye a komitin sulhu na MDD domin haka fasalin hawa kujeran na ki da kasa daya kan hau.

MDD duniya dai na cewa akwai ‘yan gudun hijiran kasar Siriya sama da miliyan 2 da dubu 400.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.