Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ingila da Jamus za su yi karawar tada kaimin Brazil 2014

A gobe Talata ake sa ran kasar Ingila za ta fafata da Jamus a wani wasan tada kaimin domin shiryawa gasar cin kofin duniya da ake tunkara a Brazil. 

'Yan wasan Ingila tare da mai horar da su Roy Hodgson a lokacin atisaye
'Yan wasan Ingila tare da mai horar da su Roy Hodgson a lokacin atisaye REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Wasa tsakanin Ingila da Jamus a da ya kasance wasa na matukar kishi tun bayan doke Jamus da Ingila ta yi a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1966 a Wembley.

Bangarorin biyu sun kara a kwannan inda suka samu nasara uku uku a tsakaninsu.

Karawar karshe ba ta yiwa Ingila dadi ba domin ta sha kashi a hanun Jamus da ci 4-1 a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.