Transparency ta fitar da sabon rahoto kan rashawa a duniya
Rahoton da kungiyar yaki da rashawa ta duniya Transparency International ta fitar, ya bayyana kasashen Afghanistan, Koriya ta Arewa da kuma Somaliya a matsayin kasashen da rashawa ta fi yaduwa, yayin da rahoton ke cewa kasashen Denmark da kuma New Zealand ne suka fi kokari wajen kawar da matsalar.
Wallafawa ranar:
Rahoton ya ce kashi 70 cikin dari na kasashen duniya ne ke fama da rashawa, kuma a cikin ma’aikatun gwamnati ne matsalar ta fi yin kamari, tare da nuna yatsa a kan jam’iyyun siyasa, ‘yan sanda, alkalan kotu da dai sauransu.
Har ila yau binciken da kungiyar da ke da mazauni a birnin Berlin na kasar Jamus ta fitar, ya bayyana cewa kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula kamar Syria, Mali da kuma Libya, sun samu koma baya a fagen yaki da rashawa.
To sai dai sakamakon komawa a kan turbar dimokuradiyya, kasashe da dama ne ke ci gaba da kokarin kawar da matsalar kamar Najeriya da kuma Myanmar a cewar Transparency International.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu