Isa ga babban shafi
Birtaniya

An samu Iska da ambaliya a Birtaniya da Faransa

Iska mai karfi da ke tafe da ruwan sama sun yi ta’adi a yankunan Birtaniya da Faransa, inda mutane hudu suka mutu tare da haifar da katsewar wutar lantarki da kuma matsaloli ga daruruwan matifiya da ke shirin bikin Kirsimeti.

Wani yanki da iska ya yi barna
Wani yanki da iska ya yi barna (©Reuters)
Talla

A yankunan Birtaniya an samu mutuwar mutane biyu a lokacin da motoci suke karo da juna saboda iska mai karfi da ke tafe da ruwan sama.

Yayin da a Faransa aka samu katsewar wutar lantarki a yankin arewa maso gabashin Britanny, inda gidaje sama da 200,000 suka kasance a cikin duhu.

A yankin Sussex da Surrey da ke kudu maso gabashin London ma gidaje da dama ne iskan ya haifar da katse masu wutar lantarki.

Iska da ruwan saman har ila yau sun tsayar da harakar sufuri musamman ma tashi da saukar jiragen sama da kuma jiragen kasa a sassan yankunan Faransa da Ingila da yankin Wales da kuma Arewacin Netherlands.

Iskan ya rusa gidaje da dama har da filin wasa na kungiyar PSV a birnin Eindhoven.
Yanayin na Iska mai karfi da ruwan sama da aka samu  ya haifar da cikas ga daruruwan mutanen Turai da ke hidimar tafiye tafiye a jajabirin Kirsemeti.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.